Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ta ce tana tsare da wata amarya wadda ta watsa wa uwargidanta tare da danta dan wata 10 tafasasshiyar miyar kubewa a jikinsu.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, CP Abdu Jinjiri ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji ta jihar.
Sai dai ya ce jajririn ya mutu sanadiyyar abin da ya faru.
CP Jinjiri, ya ce akwai rashin jituwa a tsakanin kishiyoyin.
Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba tana dakin girki ne a lokacin da uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan, sai amaryar ta fara mayar mata da magana.