Bismillahi.. Abin mamaki baya karewa. Iko sai Allah: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya.
Wani lamari mai cike da sarkakkiyar ban al'ajabi ya auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan inda amarya ta haifi sambalelen saurayi kimanin awa biyu kafin a daura mata aure.
onlinereporters.com.ng ta samu haka zalika cewa da yake tsokaci game da lamarin, angon Mista Odeolisa ya bayyana wannan al'amari da cewa daɗi kan daɗi ne. Wato alhairai biyu, a lokaci guda.
Majiyar mu dai ta labarta mana yadda lamarin ya faru inda tace abin ya farune awoyi kaɗan kafin a fara shagalin ɗaurin auren, sai kawai nakuda ta kama amaryar. Nan da nan aka mika ta asibiti inda ta haife lafiya, ta samu ɗanta namiji.
Related Posts :