• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » Dan fansho 'ya mutu ya dawo'

Dan fansho 'ya mutu ya dawo'

Wani mutum a Kazakhtan ya koma gida wata biyu bayan an yi jana'izarsa.
Mutumin wanda dan fansho ne ya koma gida ne tun kafin iyalai da 'yan uwansa su gama alhinin rasuwarsa.
"Lokacin da Baba Aigali ya shigo gida ta kofar baya cikin koshin lafiya bayan mun yi wata biyu da binne shi, 'yata mai suna Saule ta kusa mutuwa sakamakon bugun zuciya da ta gan shi," in ji Esengali Supygaliev a hirar da suka yi da jaridar Azh.kz da ake wallafawa a shafin intanet.
Mutumin mai shekara 63 ya bar gida ne da safiyar wata rana a watan Yuni kuma tun daga wancan lokacin bai koma ba. "Da ma dai an san Aigali da yawan ficewa daga gida inda yake shafe mako daya ko biyu bai koma ba ", a cewar Esengali, don haka ne iyalinsa suka jira zuwa wata daya kafin su shaida wa 'yan sanda - wadand suka nuna musu wata gawa da ta kone sosai ko za su gane shi.
Zaman makoki
Hukumomi sun ce gwajin kwayoyin halittar da aka yi kan gawar ya nuna "kashi 99.2 cikin 100 cewa ta Aigali Supygaliev ce' don haka ne aka bai wa iyalansa takardar shaidar mutuwa.
A watan Satumba iyalansa suka binne Aigali a makabartar Musulmi da ke garinsu Tomarly, kusa da kogin Caspia na Atyrau.
" Mun yi masa jana'iza sannan aka yi alhini kamar yadda ake yi a al'adance," inda abokansa suka sha shayi don nuna jimamin rashinsa, in ji Esengali.
Don haka ne lokacin da aka ga shigar gida Aigali wata biyu bayan an yi jana'izarsa sai aka soma tambayarsa abin da ya faru.
Ashe wani mutum ne da suka hadu a kasuwa a kauyen da ke makwabtaka da su ya ba shi aiki. Wata hudu da kammala aikin ne sai Aigali ya koma Tomarly.
'Yan sanda da jami'an ma'aikatar shari'a basu ce komai kan batun ba. Amma masaniyar kimiyyar da ta yi gwajin kwayoyin halitta kan gawar da aka binne ta shaida wa Azh.kz cewa tabbas kashi 99.2 na binciken ya nuna gawar ta Aigali ce ko da yake ta kara da cewa "ya kamata a sani cewa akwai kashi 0.8 na rashin tabbas".
Dangin Aigali sun bayyana bacin ransu kan batun ganin cewa tuni sun bayar da kudin kabari kamar yadda ake yi a al'adance a kasar.
Kazalika sun tambayar cewa. "Shin wanne mutum muka binne?
Posted by Unknown on Sunday, 11 November 2018 - Rating: 4.5
Title : Dan fansho 'ya mutu ya dawo'
Description : Wani mutum a Kazakhtan ya koma gida wata biyu bayan an yi jana'izarsa. Mutumin wanda dan fansho ne ya koma gida ne tun kafin iyalai ...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Dan fansho 'ya mutu ya dawo'
2018-11-11T03:08:00-08:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • Man Utd sack Mourinho after poor start to the season
    The Red Devils have won just two of their last eight matches in all competitions and sit 11 points off fourth place in the Premier League J...
  • Top 10 Richest Hausa Kannywood Actors And Actresses In Nigeria 2018
    Nigeria is a country known for it different ethnicity and tradition , one of the majority group is the Hausa. Nigeria Entertainment World is...
  • Get Etisalat 11GB at just 1700 Naira and valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 11GB data at just 1700 Naira bank payment or 1900 for recharge card  payment...
  • Bidiyon Yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti
    Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka. A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallaf...
  • Takaidattun labaran ranar Laraba 5/12/2018
    Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a hanzarta sayowa sojojin kasar nan makamai. A yau an shiga rana ta biyu da yajin aikin ma'aikatan m...
  • Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu
    Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu l...
  • "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai
    "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai ------...
  • I have better things to do with my life than being a governor, says El-Rufai
    Governor of Kaduna State, Mallam Nasir El-rufai, said that he has better things to do with his life than being the governor of Kaduna State...
  • Buhari approves NYSC, Law School for NOUN graduates
    President Muhammadu Buhari has assented to the National Open University Amendment Act, to allow the institution to operate as all other univ...
  • Get 10GB Etisalat data at just 1500 and Valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 10GB data at just 1500 Naira for bank payment or 1800 for recharge card  pay...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger