BISMILLAHI..
A wannan karon ne akayi
labarin tunawa da Sardaunar Saokoto Sir Ahmadu Bello da Kuma TAfawa Balewa
Firemiyar Nigeria na farko. Shekaru Hamsin kenan da kashesu Allah ya jikansu.
Idan na Kalli Nigeriya
tambayoyi da yawa suna zuwa zuciyata, Mutanen Nigeriya suna son tunawa da
mutanen kirki irin su sardaunar amman kuma mun gaza wajen koyi da halayensu.
Mafi yawan lokaci ina tambayar kaina da ace wanda ya rasu zai iya dawowa me zai
faru idan Sardauna ya dawo; me zai faru idan Tafawa Balewa ya dawo? Me zai faru
idan Namandi Azikwe ya dawo; me zai faru idan Awolowo ya dawo? Me zai faru idan mutane irin su Murtala
Muhammad zasu dawo da sauran dai Mutanen kirkin Nigeria da akayi gwagwarmaya
dasu.
Babu abin da zasu zo su
tarar sai dai suzo suga mutanen da suka bari basu da hadin kai, zasu zo su
tarar Arewacin Nigeria zaman lafiya yayi mata karanci. Zasu zo su rashin cin
hanci da rashawa shine kan gaba a kasar amman kuma mafi yawan jaridun kasar
basa buga labarin. Me yasa? Saboda basu suke juya akalar Jaridun ba.
A yanzu da nake muku
Magana kasashen Afrika da dama basa zaman lafiya. Me zai faru idan wadannan
mutanen kirkin suka dawo? Zasu zo su tarar muna yaki da junanmu, zasu zo su
tarar mutane Nigeria suna siyo abin da suke da arzikinsu a cikin kasar kuma
suna siyar da abin da basu dashi (Misali fetur). Zasu zo su tara da Yan
Nigeriyan da basu son Kasarsu kuma basa son junansu. Zasu zo su tarar da Yan
Nigeriyar da su su sardaunar suka sha gwagwarmaya don kada su zama bayin
turawa, wannan karon da kansu yan Nigeriyan suke zuwa kasashen turawar don suyi
bauta.

Zasu zo su tarar da yan
Nigeria wanda basa alfahari da al’adarsu, kabilarsu ko kuma abubuwan da suka
kera. Zasu zo su tarar da Yan Nijeriyan da zasu bude kamfani a cikin kasar
amman sais u dinga sanya ma abin da suke kerawa Made in China (Wato anyishi daga China). Hatta Abinci yana da sunan
turawa. Idan muka noma dankali sai muce masa Dankalin Turawa koda kuwa a Kudan
ta jihar kaduna aka nomashi. Idan mun hada biredi da kosai sai muce masa
sandswitch. Wannan sune yan Nigerian da zasu zo su tarar.
Za kuma suzo su tarar
da Yan Nijeriyan da baza fadin labarin kansu kuma basa damuwa da jin labarin
kansu; hatta gidajen jaridu sai dai su kalli CNN, Radio France, BBC, Aljazeera
da sauransu bayan muna dasu NTA, Radiyoyin Jiha, Jaridun trust da sauransu.
Zasu zo su tarar da yan Nijeriyan da basa jin dadin kansu. Idan suna son yin
Nishadi sai dai dai su Kalli Manchester United, Real Madrid, Arsenal, Barcelona
bayan muna dasu Kano Pillars, Rangers, Eyimba da sauransu.
Za kuma suzo su tarar
da yan Nijeriyan da basu damuwa da wakokin gargajiya sai dai su mayar da
hankalinsu wajen su 2pack, Shakira, Lil wayne da sauransu.
Me yasa bama tunama
kanmu da wadannan abubuwan na Zahiri ne? Hatta rashin Lafiya dan Adam yake yi
sai ya tafi America, Germany, India bayan muna da manya manyan asibitoci. Indai
baza mu canza ba babu inda zamu. Indai mun kasa tunani har abada baza mu canza
ba.
Muna da manyan Jami’oi
amman yaran masu kudi sai dai akaisu wata kasar. Muna da injiniyoyi amman
manyan hanyoyinmu da gadojinmu duk yan China ne ke yinsu. Hakan yana nufin
injiniyoyinmu ko hanya baza su iya yiba kenan? Muna da likitoci amman wasu daga
yan siyasa da masu kudi da sunji suna rashin lafiya to ya danganta ne da kasar
da mutum yake zuwa hutu. Idan kana zuwa hutu ingila ne sai kaje London, idan
kana zuwa Spain ne sai kaje Madrid don kawai a duba lafiyarka. Hakan yana nufin
bamu da imani akan akan likitocinmu kenan.
Manyan shugabanninmu
sun kirkiro da hanyar ilimi kyauta amman suna daukar yaransu suna karatu a
kasar waje. Hakan yana nufin su kansu basu yarda da makarantarmu ba kuma sun
kasa gyarawa.
To Allah dai ya kyauta.
Gashi muna son mu dinga tunawa da yan mazan jinya amman mu kanmu bamu yarda da
kawunanmu ba. Mu kanmu bamu shaidar junanmu haka abin yake akan shagabanninmu.
ALHAMDULILLAHI....
07035311650
SHARE AND COMMENT...