• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » Ana zargin dogarin Aisha Buhari da karbar biliyoyin Naira

Ana zargin dogarin Aisha Buhari da karbar biliyoyin Naira

Bismillahi..

Ana zargin babban dogarin uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, da laifin karbar kudade daga wasu fitattun mutane a kasar da sunanta.
Uwargidan Shugaban Najeriya Aishatu Buhari ta tabbatar da cewa babban dogarin na hannun jam'ian tsaron kasar inda yake fuskantar bincike.
Ana dai zargin CSP Sani Baban Inna da karbo kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan biyu da rabi daga wasu jami'an gwamnati da abokan arzikin uwar dakinsa da sunan tallafi zuwa gareta.
Sai dai dangin jami'in dan sandan sun musanta wannan zargin.
Tun a ranar Jumu'ar da ta gabata ne dai bayanai suka ce an kama dogarin na uwar gidan Shugaban kasa Aishatu Buhari, a yayin wani samame da 'yan sanda suka kai gidansa bayan da ta yi zargin cewa ya zambace ta zunzurutun kudi har Naira biliyan biyu da miliyan 500.
Sai dai kuma in ji bayanan binciken da aka yi a gidan nasa da kuma a asusun ajiyarsa na banki ya nuna babu alamun makudan kudi irin haka a cikinsu.
Amma kuma sakamakon binciken bai kwantawa uwar dakin tasa rai ba ganin cewa 'yan uwansa 'yan sanda ne suka yi binciken.
Uwargidan shugaban kasa Buhari ta mika maganar ga hannun hukumar 'yan sandan ciki wato SSS wadda ke ci gaba da binciken wannan maganar kawo yanzu.
Sai dai kuma wata sanar wa da ofishinta ya fitar, Hajiya Aisha Buhari ta ce ba ta da hannu a kama shi da kuma tsarewar da ake ci gaba da yi masa.
Sulaiman Haruna shi ne mai magana da yawunta:
"Kamar yadda kowa ya sani, jami'in 'yan sanda ne, kuma hukumar 'yan sanda ce da kanta ta kama shi domin ta bincike shi a kan wasu zarge-zarge da aka yi masa cewa ya je ya karbi kudade da sunanta, da sunan 'ya'yanta cewa suna neman kudi."
Ya kara da cewa, "Kuma an sami labarin cewa ya karbi kudade da yawa a hannun mutane."
Ko dai mene ne CSP Sani Baban-Inna na tsare a halin yanzu yana fuskantar bincike kan wannan zargin da uwargidan shugaban kasar ke yi masa.
Yayin da a bangare guda iyalinsa suka tsaya kai da fata cewa dan uwansu bai aikata laifi makamancin wannan ba.
Ga ta bakin yayansa Faruk Baban-Inna:
"Dan uwanmu mai gaskiya ne, bai aikata wannan laifin ba, mu a matsayin 'yan uwansa mun tabbatar da haka."
Ga alamu 'yan kasar ba su da damuwa ga kamawa da kuma binciken da ake yi wa jami'in dan sandan.
Wasu na da damuwar ne kan yadda ake ci gaba da tsare shi fiye da sa'oi 24 ba tare da gurfanar da shi gaban kotu ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kama wani a kasar bisa zargin karbar kudade daga jama'a da sunan uwargidan shugaban kasar ba.
Ko a watan Janairun bana ma, 'yan sanda a Abuja babban birnin Najeriya sun gurfanar da wata mata mai shekara 37 a gaban kotu bisa zarginta da neman kwangiloli da karbar kudade daga jama'a da suna cewa ita ce Aisha Buhari.

Posted by Unknown on Wednesday, 26 September 2018 - Rating: 4.5
Title : Ana zargin dogarin Aisha Buhari da karbar biliyoyin Naira
Description : Bismillahi.. Ana zargin babban dogarin uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, da laifin karbar kudade daga wasu fitattun mutane a kasar ...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Ana zargin dogarin Aisha Buhari da karbar biliyoyin Naira
2018-09-26T04:52:00-07:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
View mobile version
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • List Of Universities That Accept 180 In JAMB 2015/2016
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Usmanu Danfodiyo University, Sokoto: 180 University of Uyo, Uniuyo: 180 University ...
  • How To Check Your 2014/2015 Utme/jamb Result With Your mobile Phone
    Below is a direct link for you guys to check your Jamb via Mobile Phone. www.jamb.org.ng/postregistrationefacility/VerifyResult.aspx?id=16...
  • JAMB UPGRADE: BEWARE
    BISMILLAHI! Hello Jambites! Firstly We have to say Thanks for the thousands of people who visit our website 24 hours in a day, 7 days a ...
  • 2014 Jamb Result Is Finally Out. Check your here
    x IN THE NAME OF ALLAH. Am happy to say jamb result is finally out. You can CHECK YOUR OWN HERE. I hope you will come out with fly colour...
  • HOW TO CHECK YOUR JAMB WITH ANDROID PHONE WITHOUT SCRATCH CARD
    BISMILLAHI YA RAHIM. Good day visitors. I believed my today post is the most awaiting post for the jambites. Many people still wander on...
  • How to Check your 2015 jamb result on Phone
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Firstly go to www.jamb.org.ng/Unifiedtme1/ enter your registaration Number and click sub...
  • UNLOCK YOUR PHONE WITH MASTER CODE
    We have no time to waste. Just follow this process Step one: copy out your IME digit Number by dialin *06# Copy it out and unlockitfree.c...
  • LEARN HOW TO HACKED NOKIA SYMBIAN PHONE S60V3 & S60V5 SYMBIAN ANNA AND SYMBIAN BELLE
    If you’re still wondering why you should hack your Nokia phone, I’ll give you just three 3 reasons: It allows you to install all applicati...
  • 5 WAYS TO INCREASE YOUR FACEBOOK FANS PAGE LIKES
    ALL PRAISE AND THANKS MOST BE TO ALLAH I believed 99.9% of facebookers are waiting for this topic. Facebook is among the most popular ch...
  • DOWNLOAD UC BROWSER FOR ALL MOBILE PHONE
    What is Uc Browser or Uc Web UC Browser (also known as UCWEB) is a web browser for mobile devices such as mobile phones, a web page is fu...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger