• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » News » Dalilan da ya sa na bar gwamnatin Buhari — Ministar mata Aisha Taraba

Dalilan da ya sa na bar gwamnatin Buhari — Ministar mata Aisha Taraba

Bismillahi..

Ministar harkokin kula da al'amuran mata a Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da Mama Taraba, ta yi murabus.
Ministar ta yi murabus ne bayan da aka gaza tantance ta a cikin masu son tsayawa takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a jihar Taraba wanda za a gudanar da zaben fitar da gwani a cikinsu a ranar 30 ga watan Satumba.
A cikin wata wasika da ta rubutawa shugaban kasa a ranar 29 ga watan Satumbar 2018, Aisha Alhassan, ta ce ba a yi mata adalci ba da aka ki tantanceta a cikin 'yan takarar tun da dai ai itama ta sayi fom din takarar gwamnan kamar kowa, kuma ta kasance mai biyayya ga jam'iyyar ta APC tun shekarar 2014.
Ta shaida wa shugaban kasa a cikin wasikar cewa, ta yanke shawarar sauka daga mukaminta ne saboda rashin tantance ta da jam'iyyar ta yi a matsayin 'yar takarar gwamna a jihar Taraba.
Aisha Alhassan ta ce ' Idan har ban cancanci na tsayawa jam'iyyar APC takarar gwamna ba, to ina ganin ban cancanci kasancewa minista a gwamnatin APC ba'.
Saukarta daga mukamin nata ya zo ne kwanaki biyu bayan jam'iyyarta ta APC taki tantance ta a matsayin 'yar takarar mukamin gwamna a zaben fidda gwani da za a yi a ranar 30 ga watan Satumba.
Aisha Alhasan a lokacin da ta ke mukaminta na minista ta fito bayyanar jama'a inda ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar. shi ne ubangidanta a siyasa.
Sai dai bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bar jam'iyyar APC zuwa PDP, ministar ba ta bishi ba, inda ta hakikance cewa zata ci gaba da kasancewa a APC.
Yanzu haka dai ministar ta yanki katin zama 'yar jam'iyyar UDP a ranar Asabar ita da wasu mambobin majalisar dokokin jiharta ta Taraba su bakwai.

Posted by Unknown on Sunday, 30 September 2018 - Rating: 4.5
Title : Dalilan da ya sa na bar gwamnatin Buhari — Ministar mata Aisha Taraba
Description : Bismillahi.. Ministar harkokin kula da al'amuran mata a Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da Mama Taraba, ta yi murabu...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Dalilan da ya sa na bar gwamnatin Buhari — Ministar mata Aisha Taraba
2018-09-30T04:08:00-07:00
Unknown
News|
Newer Post
Older Post
Home
View mobile version
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • List Of Universities That Accept 180 In JAMB 2015/2016
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Usmanu Danfodiyo University, Sokoto: 180 University of Uyo, Uniuyo: 180 University ...
  • How To Check Your 2014/2015 Utme/jamb Result With Your mobile Phone
    Below is a direct link for you guys to check your Jamb via Mobile Phone. www.jamb.org.ng/postregistrationefacility/VerifyResult.aspx?id=16...
  • JAMB UPGRADE: BEWARE
    BISMILLAHI! Hello Jambites! Firstly We have to say Thanks for the thousands of people who visit our website 24 hours in a day, 7 days a ...
  • 2014 Jamb Result Is Finally Out. Check your here
    x IN THE NAME OF ALLAH. Am happy to say jamb result is finally out. You can CHECK YOUR OWN HERE. I hope you will come out with fly colour...
  • HOW TO CHECK YOUR JAMB WITH ANDROID PHONE WITHOUT SCRATCH CARD
    BISMILLAHI YA RAHIM. Good day visitors. I believed my today post is the most awaiting post for the jambites. Many people still wander on...
  • How to Check your 2015 jamb result on Phone
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Firstly go to www.jamb.org.ng/Unifiedtme1/ enter your registaration Number and click sub...
  • UNLOCK YOUR PHONE WITH MASTER CODE
    We have no time to waste. Just follow this process Step one: copy out your IME digit Number by dialin *06# Copy it out and unlockitfree.c...
  • LEARN HOW TO HACKED NOKIA SYMBIAN PHONE S60V3 & S60V5 SYMBIAN ANNA AND SYMBIAN BELLE
    If you’re still wondering why you should hack your Nokia phone, I’ll give you just three 3 reasons: It allows you to install all applicati...
  • 5 WAYS TO INCREASE YOUR FACEBOOK FANS PAGE LIKES
    ALL PRAISE AND THANKS MOST BE TO ALLAH I believed 99.9% of facebookers are waiting for this topic. Facebook is among the most popular ch...
  • DOWNLOAD UC BROWSER FOR ALL MOBILE PHONE
    What is Uc Browser or Uc Web UC Browser (also known as UCWEB) is a web browser for mobile devices such as mobile phones, a web page is fu...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger