• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » Wasu matasan Najeriya sun saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din sake tsayawa takara

Wasu matasan Najeriya sun saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din sake tsayawa takara

Bismillahi.

DA DUMIDUMINSA

Wata Kungiya Ta Siyawa Buhari Fom Din Takarar Shugaban Kasa
A Daidai Lokacin Da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yake Kasar Chana, Nan Kuma A Nijeriya Wata Kungiyar Masu Kishin Kasa Sun Siyawa Buhari Fom Din Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Ofishin Jam'iyyar APC Dake Birnin Tarayya Abuja.


Matasan na kungiyar Nigeria Ambassadors Consolidation Network sun saya wa shugaban fom din ne jim kadan bayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta fitar da kudaden da masu neman takara a jam'iyyar za su sayi fom.
Fom din shugaban kasa ne ya fi kowanne tsada, da ake sayar da shi a kan Naira miliyan 45.
To sai dai abin da mutane da dama ke mamaki shi ne yadda matasan suka sami miliyoyin kudin da suka sayawa Buhari fom din.
Bugu da kari hakan ya faru ne a daidai lokacin da wasu 'yan uwansu matasa ke korafin cewa kudin da jam'iyyar ta sanya ya yi musu tsada.
Akwai masu ra'ayin cewa matasan na rawa ne da bazar wasu manyan 'yan siyasa da suka ba su kudin sayen fom din, don a nuna cewa har yanzu Buhari yana da farin jini a wajen matasan kasar.
To sai dai shugaban kungiyar ta Nigeria Ambassadors Consolidation Network Barista Sanusi Musa ya ce ko kadan ba bu wani jami'in gwamnati da ya basu kudi.
"Bari in yi rantsuwa, Wallahi tallahi babu wani jami'in gwamnati da ya ba da ko kwabo a kudin da muka biya," in ji Sanusi Musa.
Ya kara da cewa, matasan sun kai shekara guda suna tara kudi domin saya wa shugaban fom.
"Mutum daya ne, wani dan kasuwa dan kabilar Ibo kadai ya kawo mana gudunmuwar Naira miliyan biyar, da ya ji abin da muke shirin yi," in ji shi.
A cewarsa sun gamsu da irin shugabancin Buhari, don haka ne suka yanke hukuncin mara masa baya a zaben da ke tafe.
A zaben shekarar 2015 ma Muhammadu Buhari ya samu gudunmuwa daga 'yan kasar da dama wajen saya masa fom din takara da kuma kudin yakin neman zabe.
Sai dai wasu suna ganin da wuya a wannan karon ya samu irin wannan gudunmuwar, kasancewar wasu 'yan kasar sun dawo daga rakiyarsa.
Wannan tunanin da wasu 'yan kasar ke yi na daga dalilan da Sanusi Musa ya bayyana cewa suka saya wa Buhari fom din, domin nuna wa jama'a cewa har yanzu matasa suna goyon bayan Buhari.
A shekarar 2014 dai kwamitin yakin neman zaben Shugaba Buhari ya fitar da wani kati wanda jama'a za su iya amfani da shi wajen ba wa Buhari gudunmuwa.
To sai dai babu tabbas ko a wannan karon ma za a yi amfani da wannan hanyar.
Kuma idan ma za a yi din shin jama'a za su bayar da gudunmuwa irin yadda suka bayar a baya?
Posted by Unknown on Thursday, 6 September 2018 - Rating: 4.5
Title : Wasu matasan Najeriya sun saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din sake tsayawa takara
Description : Bismillahi. DA DUMIDUMINSA Wata Kungiya Ta Siyawa Buhari Fom Din Takarar Shugaban Kasa A Daidai Lokacin Da Shugaban Kasa Muhammadu Buh...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Wasu matasan Najeriya sun saya wa shugaban kasar Muhmmadu Buhari fom din sake tsayawa takara
2018-09-06T03:31:00-07:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
View mobile version
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • List Of Universities That Accept 180 In JAMB 2015/2016
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Usmanu Danfodiyo University, Sokoto: 180 University of Uyo, Uniuyo: 180 University ...
  • How To Check Your 2014/2015 Utme/jamb Result With Your mobile Phone
    Below is a direct link for you guys to check your Jamb via Mobile Phone. www.jamb.org.ng/postregistrationefacility/VerifyResult.aspx?id=16...
  • JAMB UPGRADE: BEWARE
    BISMILLAHI! Hello Jambites! Firstly We have to say Thanks for the thousands of people who visit our website 24 hours in a day, 7 days a ...
  • 2014 Jamb Result Is Finally Out. Check your here
    x IN THE NAME OF ALLAH. Am happy to say jamb result is finally out. You can CHECK YOUR OWN HERE. I hope you will come out with fly colour...
  • HOW TO CHECK YOUR JAMB WITH ANDROID PHONE WITHOUT SCRATCH CARD
    BISMILLAHI YA RAHIM. Good day visitors. I believed my today post is the most awaiting post for the jambites. Many people still wander on...
  • How to Check your 2015 jamb result on Phone
    BISMILLAHI.... THE LORD OF RASULULLAHI (S.AW). Firstly go to www.jamb.org.ng/Unifiedtme1/ enter your registaration Number and click sub...
  • UNLOCK YOUR PHONE WITH MASTER CODE
    We have no time to waste. Just follow this process Step one: copy out your IME digit Number by dialin *06# Copy it out and unlockitfree.c...
  • LEARN HOW TO HACKED NOKIA SYMBIAN PHONE S60V3 & S60V5 SYMBIAN ANNA AND SYMBIAN BELLE
    If you’re still wondering why you should hack your Nokia phone, I’ll give you just three 3 reasons: It allows you to install all applicati...
  • 5 WAYS TO INCREASE YOUR FACEBOOK FANS PAGE LIKES
    ALL PRAISE AND THANKS MOST BE TO ALLAH I believed 99.9% of facebookers are waiting for this topic. Facebook is among the most popular ch...
  • DOWNLOAD UC BROWSER FOR ALL MOBILE PHONE
    What is Uc Browser or Uc Web UC Browser (also known as UCWEB) is a web browser for mobile devices such as mobile phones, a web page is fu...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger