• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

BISMILLAHI..
Katafaren shafin sada zumunta na Facebook ya sake yin wata hobbasa, inda ya bullo da fasahar bidiyo, da za ta yi gogayya da YouTube da kuma tasoshin Talbijin.
Nan gaba kadan masu amfani da Facebook za su ga sabon madannin Kallo, wanda zai ba su damar ganin shirye-shirye iri daban-daban, wasu daga ciki kamfanin ne ke daukar nauyinsu.
Madannin mai suna 'Watch' zai dace da bukatun mutum, ta yadda mai amfani da Facebook zai iya gano sabbin shirye-shirye, bisa la'akari kan abin da abokansa suke kallo.
Masu kallo za kuma su iya ganin sharhi da kuma haduwa da abokansu, har ma su hada wani rukunin abokai don kallace-kallace.
"Kallon wani nuni ba zai kasance, wani abu da ba hannun mai kallo ba," a cewar mutumin da ya assasa kamfanin, Mark Zuckerberg a wani bayani da ya wallafa a Facebook.
"(Fasahar) ka iya ba da damar musayar wata gogayya da kuma tattaro mutanen da suka damu da wasu abubuwa waje guda."
Tsawon wani lokaci Facebook yana da fasahar bidiyo a shafinsa, sai dai har zuwa yanzu, faya-fayen bidiyon da ba na kwararru ba, da kuma takaitattun shirye-shiryen kafofin yada labarai ne suka fi mamayewa.
A bara ne, katafaren kamfanin Facebook ya kara madannin bidiyo, inda kuma ya nuna cewa zai iya yin wani yunkuri don samar da shirye-shirye na ainihi.

Fasahar Kallo ta Facebook za ta iya bude sabuwar kofar samun kudin shiga ga kamfanin da kuma masu watsa shirye-shirye, yayin da masu kallo za su iya ganin tallace-tallace kafin da kuma a cikin wasu shirye-shirye da ake nunawa.
Sharhin Leo Kelion, editan sashen Fasaha na BBC
Facebook ya ce yana fata fasahar shirye-shiryensa ta bidiyo za ta biya bukatun wani kebantaccen fannin rayuwa da kuma na daukaci.
Idan zabin da aka kaddamar wani abin misali ne, to fasahar za ta mayar da hankali kan shirye-shiryen nishadantarwa na rayuwar zahiri ciki har da girke-girke, da shirin tabbatar da koshin lafiya, da shirin tafiye-tafiye, wadanda za su fi dacewa a kan wayoyin zamani, maimakon shahararrun wasannin kwaikwaiyo da fina-finai wadanda masu tsadar shiryawa kuma sun fi dacewa da talbijin inda mai kallo zai iya yin waiwaye.
Cunkushewar kasuwa
Facebook na shiga kasuwar da take kara zama mai sarkakiya da cunkoso, inda za ta goga kafada da tasoshin talbijin na asali gami da shafukan bidiyo na intanet kamar YouTube da Netflix.
A ranar Laraba, kamfanin Disney ya ba da sanarwar cewa daga shekara ta 2019, zai fice daga yarjejeniyar da ya sa hannu da Netflix, inda zai bullo da fasahar yada shirye-shiryensa kai tsaye ga jama'a.

Zai kuma bullo da hanyar yada shirye-shiryen wasanni na ESPN shekara mai zuwa.
Tun tuni Facebook na da jerin shirye-shirye da suka hadar da gasar kwallon kwando a Amurka da gasar kwallon kwandon mata da shirye-shiryen kula da yara da wani shirin rayuwar namun daji daga National Geographic.
Fasahar 'Watch' za ta takaita ne a Amurka kafin ta fita ta kara bazuwa.

Posted by Unknown on Sunday, 13 August 2017 - Rating: 4.5
Title : Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin
Description : BISMILLAHI.. Katafaren shafin sada zumunta na Facebook ya sake yin wata hobbasa, inda ya bullo da fasahar bidiyo, da za ta yi gogayya d...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin
2017-08-13T04:04:00-07:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • Man Utd sack Mourinho after poor start to the season
    The Red Devils have won just two of their last eight matches in all competitions and sit 11 points off fourth place in the Premier League J...
  • Top 10 Richest Hausa Kannywood Actors And Actresses In Nigeria 2018
    Nigeria is a country known for it different ethnicity and tradition , one of the majority group is the Hausa. Nigeria Entertainment World is...
  • Takaidattun labaran ranar Laraba 5/12/2018
    Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a hanzarta sayowa sojojin kasar nan makamai. A yau an shiga rana ta biyu da yajin aikin ma'aikatan m...
  • Get Etisalat 11GB at just 1700 Naira and valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 11GB data at just 1700 Naira bank payment or 1900 for recharge card  payment...
  • Bidiyon Yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti
    Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka. A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallaf...
  • Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu
    Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu l...
  • Na san masu yi min fatan mutuwa — Buhari
    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017. Shugaban ya bayyana haka...
  • "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai
    "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai ------...
  • I have better things to do with my life than being a governor, says El-Rufai
    Governor of Kaduna State, Mallam Nasir El-rufai, said that he has better things to do with his life than being the governor of Kaduna State...
  • Buhari approves NYSC, Law School for NOUN graduates
    President Muhammadu Buhari has assented to the National Open University Amendment Act, to allow the institution to operate as all other univ...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger