Bismillahi..
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
wanda ya shafe fiye da wata uku yana jinya a Landan, ya ce yana samun
sauki kuma zai koma gida ne kawai idan ya samu amincewar likitocinsa, in
ji kakakinsa Malam Garba Shehu.
A ranar Asabar ne shugaban ya gana wasu hadimansa a gidan da yake jinya a birnin Landan.
Cikin
wadanda suka gana da shugaban har da Ministan Yada Labaran kasar Lai
Mohammed da Malam Garba Shehu da Mista Femi Adesina da sauransu.
Garba Shehu ya ce: "Buhari ya murmure kuma yana samun kyakykyawar ci gaba.
Title : Zan koma Nigeria bayan samun yardar likitocina – Buhari
Description : Bismillahi.. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya shafe fiye da wata uku yana jinya a Landan, ya ce yana samun sauki kuma z...