• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » 'Yan kwadago sun yi watsi da karin albashi

'Yan kwadago sun yi watsi da karin albashi

Kungiyar kwadagon Najeriya ta yi watsi da albashi mafi karanci da gwamnoni suka kara daga N18,000 zuwa N22,500.
Kungiyar ta ce ta dauki mataki ne saboda a alkawarin da suka yi da gwamnonin a baya sun ce N30,000 za su kara a matsayin albashi mafi karanci.
Ranar Talata gwamnonin suka amince da matakin karin albashin a wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja bayan matsin lamba daga kungiyoyin kwadago.
Shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan jihar Zamfara, Abdul'ziz Yari Abubakar ya ce ba adadin kudin kawai suka yi la'akari da shi ba har da duba tsarin samun zarafin iya biyan albashin.
Sai dai kuma kungiyar kwadago ta kalubalanci matakin da gwamnonin suka dauka wanda ta ce ya saba wa yarjejeniyar da suka amince ta biyan N30,000 ga karamin ma'aikaci.
Kungiyar ta ce tana kan bakanta na shiga yajin aiki a ranar 6 ga watan Nuwamba idan gwamnonin suka ki amincewa da bukatunta.
Jami'in tsare-tsare na gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya, Kwamared Nasir Kabir, ya shaida wa BBC cewa za su tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani idan har gwamnati ba ta amince da bukatunsu ba.
Ya kuma ce sun riga sun shirya, tare da sanar da mambobinsu matakin da suke shirin aiwatarwa.

Posted by Unknown on Wednesday, 31 October 2018 - Rating: 4.5
Title : 'Yan kwadago sun yi watsi da karin albashi
Description : Kungiyar kwadagon Najeriya ta yi watsi da albashi mafi karanci da gwamnoni suka kara daga N18,000 zuwa N22,500. Kungiyar ta ce ta dauki mat...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
'Yan kwadago sun yi watsi da karin albashi
2018-10-31T06:02:00-07:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • Man Utd sack Mourinho after poor start to the season
    The Red Devils have won just two of their last eight matches in all competitions and sit 11 points off fourth place in the Premier League J...
  • Top 10 Richest Hausa Kannywood Actors And Actresses In Nigeria 2018
    Nigeria is a country known for it different ethnicity and tradition , one of the majority group is the Hausa. Nigeria Entertainment World is...
  • Get Etisalat 11GB at just 1700 Naira and valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 11GB data at just 1700 Naira bank payment or 1900 for recharge card  payment...
  • Bidiyon Yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti
    Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka. A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallaf...
  • Takaidattun labaran ranar Laraba 5/12/2018
    Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a hanzarta sayowa sojojin kasar nan makamai. A yau an shiga rana ta biyu da yajin aikin ma'aikatan m...
  • Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu
    Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu l...
  • "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai
    "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai ------...
  • I have better things to do with my life than being a governor, says El-Rufai
    Governor of Kaduna State, Mallam Nasir El-rufai, said that he has better things to do with his life than being the governor of Kaduna State...
  • Buhari approves NYSC, Law School for NOUN graduates
    President Muhammadu Buhari has assented to the National Open University Amendment Act, to allow the institution to operate as all other univ...
  • Get 10GB Etisalat data at just 1500 and Valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 10GB data at just 1500 Naira for bank payment or 1800 for recharge card  pay...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger