Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta yi a 2015.
'Yan bindiga cikin kakin soji sun kashe shanun makiyaya fiye da 150 a Taraba.
Wani jami'in NSCDC a jihar Borno ya harbe matsarsa da wasu 'yan uwansa biyu kafin ya kashe kansa.
Ba bu wani dan siyasa mai hankali da zai watsi da masu sana'ar nishadantarwa - Osinbajo.
Biyafra ta zargi Atiku da yunkurin yin amfani da 'yan kabilar Igbo domin cimma burinsa.
Lauyoyi za su maka gwamnatin Kano a Kotu saboda amfani da yara wajen zanga-zanga.
Hukumar sojojin kasa za ta fara kera motocin yaki a Najeriya.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci 'yan Najeriya da ka da su zabi duk wanda ya gaza gabatar da takardun kammala karatunsa.
Shugaban APC a Enugu ya tsallake rijiya da baya a hannun wasu makasa.
'Yan firamare 2 sun bace bayan zanga-zangar goyon bayan Ganduje a Kano.
Kasar Saudiyya ta ce za ta hukunta dukannin wadanda ke hannu a mutuwar Jamal Khashoggi.
Iran ta fusata kan ziyarar Netanyahu a Umman.
Shugabar gwamnatin Jamus,Ankela Merkel ta bayyana cewa, kasarta ba za ta sake siyar wa Saudiyya makamai ba.
EPL: Liverpool ta ci Crystal Palace 4:1 a wasan jiya.
EPL: Leicester City da West Ham United sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Title : Taqaitattun Labaran Safiyar Lahadi 28/10/2018
Description : Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta yi a 2015. 'Yan bindiga cikin kakin soji sun kashe shanun makiyaya fiye da 150...