• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » Yadda kafofin sada zumunta suka kashe min aure'

Yadda kafofin sada zumunta suka kashe min aure'

Ya za ki ji idan aka ce kafofin sada zumunta na zamani sun yi sanadiyyar mutuwar aurenki ko na wata 'yar uwarki ko kawarki?
Za ki iya tuna sau nawa wani ya tura miki wani rubutaccen sako ko hoto ko bidiyo na batsa ko kuma ya yi miki wata magana da ba ta kamata ba?
Kawaye ko 'yan uwanki nawa za ki iya tunawa da suka ba ki labarin cewa an taba cin zarafinsu ta kafofin sada zumunta?
Wannan shi ne yanayin da mata da dama suke rayuwa a ciki sakamakon amfani da kafofin sada zumunta na zamani.
Babu shakka al'amuran zamantakewa sun inganta ta wani fannin, mu'amala tsakanin jama'a ta inganta, nesa ta zama kusa ga 'yan uwa da abokan arziki, duk sakamakon kafofin sada zumunta na intanet.
Baya ga saukin sarrafawa, ana iya amfani da kafofin wajen tura rubutu ko hoto ko bidiyo tsakanin mutum biyu, abin da hakan ke bayar da damar wani abu da ba za a so jama'a su gani ba, in ban da wanda aka tura wa.
Kunya da kawaici da kuma gudun zargi na daga abubuwan da suke hana mata da dama fitowa su bayyana irin wadannan sakonnin da ake tura musu, ko da kuwa ransu bai so ba.
Wasu matan suna samun irin wadannan sakwonni daga 'yan uwa na jini, ko makota, ko abokan karatu ko ma abokan aiki, ko da kuwa dokokin aikin sun hana cin zarafin abokan aiki ta kowace hanya.
Sau da dama dai, irin wadannan sakwonnin da ake tura wa mata suna janyo rashin yarda tsakanin ma'aurata, da sanya zargi daga iyaye ko jama'a ga duk wata da aka ga tamkar tana da alaka da wannan sako.
Hausawa na cewa mutunci madara ne, in ya zube shi ke nan.
Irin wannan ne ya haifar wa wata mata a Ghana babbar matsala tsakaninta da mijinta, zargi ya yi yawa tsakaninsu, har ya kai yana kulle ta a gida, yana yi mata duka saboda zargi, daga karshe ma auren ya rabu.
Da wannan matar ce filin Adikon Zamani na wannan mako ya tattauna domin jin ainihin abin da ya faru da ita.

Posted by Unknown on Saturday, 20 October 2018 - Rating: 4.5
Title : Yadda kafofin sada zumunta suka kashe min aure'
Description : Ya za ki ji idan aka ce kafofin sada zumunta na zamani sun yi sanadiyyar mutuwar aurenki ko na wata 'yar uwarki ko kawarki? Za ki iya t...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
Yadda kafofin sada zumunta suka kashe min aure'
2018-10-20T06:36:00-07:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • Man Utd sack Mourinho after poor start to the season
    The Red Devils have won just two of their last eight matches in all competitions and sit 11 points off fourth place in the Premier League J...
  • Top 10 Richest Hausa Kannywood Actors And Actresses In Nigeria 2018
    Nigeria is a country known for it different ethnicity and tradition , one of the majority group is the Hausa. Nigeria Entertainment World is...
  • Get Etisalat 11GB at just 1700 Naira and valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 11GB data at just 1700 Naira bank payment or 1900 for recharge card  payment...
  • Bidiyon Yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti
    Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka. A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallaf...
  • Takaidattun labaran ranar Laraba 5/12/2018
    Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a hanzarta sayowa sojojin kasar nan makamai. A yau an shiga rana ta biyu da yajin aikin ma'aikatan m...
  • Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu
    Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu l...
  • Na san masu yi min fatan mutuwa — Buhari
    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017. Shugaban ya bayyana haka...
  • "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai
    "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai ------...
  • I have better things to do with my life than being a governor, says El-Rufai
    Governor of Kaduna State, Mallam Nasir El-rufai, said that he has better things to do with his life than being the governor of Kaduna State...
  • Get 10GB Etisalat data at just 1500 and Valid for a month
    BISMILLAHI.. This is unbeliable. You can now enjoy etisalat 10GB data at just 1500 Naira for bank payment or 1800 for recharge card  pay...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger