Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Hukumar zabe na kasa na INEC ta fitar da jerin ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Adamawa a dalilin korafe-korafen da ake yi game da Gwamna Jibrila Bindow.
Ana ta kishin-kishin din cewa Jam’iyyar APC ba za ta tsaida Muhammad Jibrila Bindow a matsayin ‘Dan takaran ta na Gwamna a Jihar Adamawa ba saboda zargin rashin isassun takardun Boko na kammala karatun Sakandare.
Yanzu dai Hukumar INEC ta fitar da jerin ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Adamawa dauke da matakin ilmin kowane ‘Dan takara inda aka ga cewa ba a samu Gwamna mai-ci Jibrila Bindow na APC da shaidar jarrabawar WAEC ba.
INEC ta bayyana cewa Jibrila Bindow ya mika mata takardar kammala Sakandare ne daga Makarantar Miango a maimakon shaidar jarrabawar WAEC. Kowane ‘Dan takara dai ya mikawa Hukuma akalla takardar sa na WAEC illa Gwamnan.
Idan ba ku manta ba, kwanan nan ne dai wata Kungiya mai zaman kan-ta ta maka Gwamna Jibrila Bindow kara a gaban wani babban Kotun Tarayya da ke Abuja inda ta ke zargin sa da badakala a jarrabawar WAEC ta kammala Sakandare.
A baya Hukumar WAEC ta ce takardar da ta mikawa Shugaba Buhari ba asalin sakamakon jarrabawar sa bane, WAEC tace idan mutum ya rasa ainihin sakamakon sa ne sai a ba sa irin wannan takarda a madadi.
Title : Badakalar WAEC: An rasa takardun Gwamnan Adamawa Bindow
Description : Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Hukumar zabe na kasa na INEC ta fitar da jerin ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Adamawa a dalili...