• About
  • Sitemap
  • Privacy and Policy
  • Facebook
  • Contact Us
ONLINE REPORTERS
  • Home
  • TUTORIALS
    • Blogging
    • Download
    • News
    • Others
  • Online Money
    • Social Media
    • Mobile Tips
  • Nokia tutorials
  • Free Browsing
  • Computer
  • Android
Home » Hausa » YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA

YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA

Daga Datti Assalafy

Lokacin da Maigirma Sanata Kabiru Marafa ya bada tallafinshi Naira miliyon shida da sauran kudin da jama'ar Nigeria suka tallafa aka hada kudin ya kai Naira miliyon goma sha biyar, sai aka kira wadanda sukayi garkuwa da tagwayen aka sanar musu cewa kudin ya cika kamar yadda sukace a biyasu kafin su saki tagwayen, bayan an sanar da su cewa kudin ya cika sai sukace to a jirasu zasu kira don a kai musu kudin.

Bayan kamar awa uku sai suka kira wayan Ibrahim mijin yayarsu wanda ake sasantawa da shi, sukace a dauko kudin azo wani gari da ake kira Gurbin-Burai inda kwanaki masu garkuwa da mutane sukayi kashe-kashe da kone-kone sukace idan an isa garin a kirasu, kafin su Ibrahim su isa garin masu garkuwa da tagwayen suna ta kiransu a waya cewa mai yasa har yanzu ba su iso ba? sun gaji da jira, su fa zasu kashe tagwayen suyi tafiyarsu sai dai azo a dauki gawarsu, Ibrahim dai yayi ta basu hakuri yana cewa mun kusan isowa.

Bayan su Ibrahim sun isa garin na Gurbin-Burai suka kira masu garkuwan aka fada musu cewa sun iso garin, sai sukace to daga nan su biyo ta wani kauye da ake kira Dumburum daga Dumburum daji za'a shiga, to su Ibrahim sai suka ajiye motarsu suka nemi mashina guda uku, sai masu garkuwan suka kira waya sukace ai mun ganku ko taho garin na Dumburum zamu fada muku hanyar da zakubi ta kawoku cikin jeji inda muke, jama'a kunga wannan ya nuna cewa akwai masu yiwa 'yan bindigar leken asiri ko ta ina a cikin wadannan garuruwa na Zamfara.

Daga garin Dumburum su Ibrahim sunyi tafiya kamar tsawon kilo mita 15 a cikin jeji, suna cikin tafiya kawai sai suka fara ganin mutane da bindigogi suna ta bullowa wanda yawansu ya kai kusan mutum dari da hamsin, kuma kowa rike yake da bindiga kirar AK47 ana cewa su dakata a gurin, sai su Ibrahim suka dakata suka sauka daga kan mashina, da ma su uku ne, da shi Ibrahim mijin yayarsu, da wanda zai auri Hussaina, da babban yayansu, sai Ibrahim ya dauko kudin ya ajiye a gabansa wanda aka zuba kudin a cikin jaka guda biyu, 'yan bindigar sun gewayesu a tsakiyar jeji, bayan kamar mintuna biyu sai ga shugaban kuma ogan 'yan bindigar ya bullo tare da tawagarsa rike da manyan bindigogi tagwayen suna bayanshi.

Haka shugaban barayin ya matso har kusa da Ibrahim inda kudin suke ajiye a cikin jaka a 'kasa, bai ce masa komai ba sai yayi umarni da wasu yaranshi guda biyu su bude jakan su kirga kudin, bayan sun kammala kirga kudin gaba daya ya cika miliyon 15, sai ogan yace a mayar da kudin cikin jaka a daure, da akayi haka, sai ogan barayin ya tsuguna a gaban kudin ya debi kasa da hannunshi ya watsa akan jakakkunan kudin, sai ya mike tsaye ya hau kan jakakkunan kudin da kafafunshi, sai ya daga kanshi sama yana karanta wasu 'dalasimai irin na tsafi, yana tayi har kusan kamar mintuna 2 sai ya saukar da kanshi kasa, ya kuma sauka daga jakar kudin ya ja da baya, sai yayi umarni ga yaranshi da su dauki kudin, sai suka dauka, sai ya kalli Ibrahim yayi dariya sai yace sannunku da zuwa ashe kuna son kannenku.

Sai Ibrahim ya amsa masa, sai yace ai ba wanda baya son kannenshi oga, daga nan sai yayi umarni da a kawo tagwayen ya mikasu ga Ibrahim yace su juya su tafi kar su kuskura su juya baya, Ibrahim yace mun gode oga, shine suka dauko tagwayen suka iso har kauyen Gurbin-Burai inda motarsu take, daga nan sai Ibrahim ya fara kiran waya suna sanar da 'yan uwa da wadanda suka tallafa cewa tagwayen sun kubuta lafiya.

Jama'a wannan shine bayanin abinda ya faru game da yadda akaje aka karbo tagwayen.
Abinda bincikenmu ya tabbatar mana shi ne an jima ana bibiyar tagwayen domin ayi garkuwa da su, mutane da dama suna da hannu a cikin garkuwa da 'yan matan, wato nazarin da mukayi a kai shine wadannan masu aikata laifin garkuwa da mutane sun kawo wata sabuwar hanyar yin garkuwa da mutane ta hanyar bibiyar mutanen da suke mu'amala da dandalin sada zumunta na zamani musamman wadanda suke watsa hotunansu a social media, masu garkuwan suna la'akari da farin jinin wanda yake social media da yawan jama'ar da suke tare da shi wanda idan sunyi garkuwa da shi dole za'a biyasu kudi.

Kunga wadannan tagwaye babban abinda yayi sanadiyyar jefa su cikin wannan bala'i shine saka hotunansu da suke yi a social media da irin yadda ake kambamasu, wadanda sukayi garkuwa da su sun dauki lokaci mai tsawo suna bin diddiginsu har zuwa ranar da tagwayen suka ziyarci garin Mahaifinsu domin su raba katin aurensu, garin kauye ne, a daren ranar da za'ayi garkuwa da su tun isarsu garin suke ta yawo, kuma duk inda suka wuce sai an nunasu, da dare yayi misalin karfe 11 da wasu mintuna akaje gidan kawarsu da suka sauka zasu kwana aka sacesu gaba daya, har da kanin mijin kawar tasu, da ita kawar tasu aka tafi dasu jeji.

Muna nazarin ayyukan masu garkuwa da mutane da dabarunsu, mun sani cewa idan masu garkuwa da mutane sun kama mutum biyu ko sama da haka, to ba sa yarda su sake daya ko biyu su bar wani, a'a sai dai su sakesu gaba daya, to amma wannan sun kamasu gaba daya, sai suka saki tagwayen sauran kuma ba'a sakesu ba, wannan zai tabbatar maka da cewa masu garkuwan sunyi karfin da ya wuce tunanin duk wani mai tunani ko hasashe da nazari, kuma wannan babban kalubale ne ga gwamnatin Nigeria, mahukunta sai sunyi da gaske imba haka ba masifar zata mamaye jihohi da dama a Nigeria.

Daga karshe ina kira ga 'yan mata da mazaje masu yada hotunansu a kafofin sada zumunta kuma suke da dunbin masoya da suyi taka tsantsan, sannan su kiyaye sirrin tsaron kawunansu, ku dena bayyana inda zakuje idan zakuyi tafiya, bayyanawan hatsari ne mai girma a irin wannan lokaci da muka tsinci kanmu, a dinga 6atar da kafa idan za'ayi tafiya ko za'a dawo daga tafiya.

Muna rokon Allah Ya tsaremu daga dukkan sharri da makirci da mugun tarko.
Yaa Allah duk masu bibiyarmu da sharri lo cutarwa Allah Ka mayar da sharrin da cutarwan zuwa kansu Amin.

Posted by Unknown on Saturday, 24 November 2018 - Rating: 4.5
Title : YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA
Description : Daga Datti Assalafy Lokacin da Maigirma Sanata Kabiru Marafa ya bada tallafinshi Naira miliyon shida da sauran kudin da jama'ar Nigeria...

Share this post on

Facebook Google+ Twitter
YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA
2018-11-24T00:32:00-08:00
Unknown
Hausa|
Newer Post
Older Post
Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Followers

SUBSCRIBE our Daily Posts for free

Enter your email address:

Delivered by FeedBurner

Auto Add

Labels

Android Blogging Computer Download Free Browsing Gossip Hausa Internet Islam Lifestyle Mobile Tips Music Must Read News Nokia tutorials Online Money Others Social Media sports

SEARCH ENGINE

SUBSCRIBE OUR DAILY UPDATES FREE

Subscribe our free daily updates

 Subscribe to Our RSS Feed
Get this widget Now

Google Translate

Popular Posts

  • Man Utd sack Mourinho after poor start to the season
    The Red Devils have won just two of their last eight matches in all competitions and sit 11 points off fourth place in the Premier League J...
  • I have better things to do with my life than being a governor, says El-Rufai
    Governor of Kaduna State, Mallam Nasir El-rufai, said that he has better things to do with his life than being the governor of Kaduna State...
  • Bidiyon Yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti
    Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka. A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallaf...
  • What Cristiano Ronaldo did when Real Madrid stopped following him on social media amid airbrushing claims
    Cristiano Ronaldo completed a £100million transfer from Real Madrid to Juventus in the summer ending his nine-year tenure at the Bernabeu. ...
  • Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu
    Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu l...
  • Buhari approves NYSC, Law School for NOUN graduates
    President Muhammadu Buhari has assented to the National Open University Amendment Act, to allow the institution to operate as all other univ...
  • Top 10 Richest Hausa Kannywood Actors And Actresses In Nigeria 2018
    Nigeria is a country known for it different ethnicity and tradition , one of the majority group is the Hausa. Nigeria Entertainment World is...
  • El-Rufai drags ABU, KadPoly to court over N9.50bn unremitted taxes
    Kaduna State Government, through its Board of Internal Revenue, has taken two federal government institutions domiciled in the state, Ahmadu...
  • Na san masu yi min fatan mutuwa — Buhari
    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017. Shugaban ya bayyana haka...
  • "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai
    "Za mu wayar wa mutane kai kan zaben mutane nagari ba munafukai, barayi da wadanda ba su iya yi wa kan su aski" - El-Rufai ------...

GOOGLE INDEX


About Me

Unknown
View my complete profile
Copyright © 2016 ONLINE REPORTERS - All Rights Reserved
Design by MUJAHEED NASEER - Blogger Templates - Powered by Blogger